<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>230</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Albarka tana kan mutum wanda bai ratse ba,
 Wanda bai tsaya a hanya ta masu zunubi ba.

[V2]
 2) A wurin masu ba'a, shi ba ya kan zauna ba,
 Maganar Allah ya ke bi dare da rana kuwa.

[V3]
 3) Misalin itace ne shi a bakin ruwaye,
 Zai ba da ƴaƴa lotonsa, yaushi kuwa ba ya yi.

[V4]
 4) Duk aikinsa da ya ke yi, albarka tana kai.
 Miyagu kamar ƙaiƙai ne, iska zai ture su.

[V5]
 5) Ranar shari'a, miyagu ba za su tsaya ba,
 Ko kuwa su masu zunubi a gidan adalai.

[V6]
 6) Ubangijinmu kuwa ya san tafiyar adalai.
 Amma tafarkin miyagu lalle zai lalace.</lyrics>
<title>Albarka Tana Kan Mutum Wanda Bai Ratse Ba LW230</title>
</song>